Iyalen Marigayi mai shara’a Idris Kutigi sun bayyana ranar jana’izar sa.

Read Time:52 Second

A wata sanarwa da Babar yar marigayin Binta Aliyu ta fitar ranar talata tace gawar marigayin zai iso Abuja daga birnin London ranar Laraba da safe , sai kuma ayi jana’izar baban lawyan a ranakun Ashirin da Hudu da kuma Ashirin da biyar.
Sanarwa ta kara da cewa za’a binne shi a makabartan Gudu dake Abuja bayan anyi masa sallah a Baban masallacin Abuja.
Za a gudanar da Addu’ar Fidau a gidan marigayi baban mai shara’a a dake Asokoro Abuja ranar Alhamis da large Goma na safe .
Kuma za a gudanar da addu’ar fidau a fadar Esu Nupe a Bida da kuma Kutigi a jihar Niger.
Marigayi Kutigi baban lawya ne kuma Alkali. Ya taba rike matsayin komishinan shara’a na jihar Niger kafin ya zama Alkalin a baban kotun tarayya. Ya zama Alkalin kotun kolin Najeriya a shekara ta 1992 kana ya zama shugaban Alkalen Najeriya a ranar talatin ga watan junairu, 2003 harzuwa watan Disamba na 2009.
Marigayin ya mutu a Daren asabar a wani Asibiti dake birnin London, yana da shekara 75.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %