Ana zargin wani fasto da wasu mutane biyu da kashe wata ma’aikaciyar jinya a makurdi.

Read Time:44 Second

Baban kotun majistiri ta daure wani fasto Sabastine igwe , James Akpa da Michael Ochigo saboda laifin kashe wata ma’aikaciyar jinya a makurdi baban birnin jihar Benuwe.
Jami’in da ya shigar da kara ASP Edward IMO ya shaidawa kotun cewa faston da sauran mutum biyun sun kashe ma’aikaciyar jinyar ce a wani kauyen Anwu kusa da makurdi.
IMO ya kara da cewa an dauke karar daga hedkwatar Yan sanda na Obusa zuwa ofishin jami’an bincike da leken atsiri na jihar a ranar goma sha bakwai ga watan Oktoba.
Amma kuma roko da masu laifin sukayi bai karbu ba saboda rashi hurumi.
Laifuffukan sun sabawa sashe ne 97 da Dari biyu da Ashirin da biyu na dokar aika ta laifi na jihar Benuwe da aka yiwa gyara.
Alkalin kotun majistirin Mr Isaac Ajim ya daga karar zuwa ranar Ashirin da shida ga watan Nuwamba don cigaba da saurara.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %