Harkokin kasuwanci ya fara kankama bayan fadan Kaduna.

Read Time:32 Second

A ranar Alhamis harkokin hada hada sun fara gudana a cikin garin Kaduna bayan a sassauta dokar hana fita na awa Ashirin da Hudu bayan rikicin ranar Lahadi.
Dokar ta takura harkoki a cikin garin Kaduna da kewayen ta saboda rikicin dayayi ajalin mutane Ashirin da uku, goma sha bakwai suka jikkata an kuma kona dukiyoyi da yawa.
An bude shaguna a Babar kasuwar Abubakar Gumi haka ma Bankuna da makarantu sun bude.
Sai dai kuma yawancin shagunar sayarda kayayyakin mota Dana Babur dake layukan Ahmadu Bello,Lagos street, Ibadan , Abekuota da katsina street suna kulle haryanzu.
Ana Iya ganin jami’an tsaro a kusa da guraren.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %