Kungiyar kiristoci na kasa CAN ta bukaci Gwamnatin tarayya ta bankado keyar wadanda suka haddasa rikicin Kaduna.

Read Time:54 Second

Kungiyar kiristocin Najeriya tayi kira ga gwamnatin tarayya Dana jihar Kaduna da su kawo karshen rashin hukumta masu laifi ta hanya kamo wadanda suka haddasa rikicin Kaduna don hukumta su.
Kungiyar CAN ta bayyana kaduwarta dangane da yadda wasu masu sace mutane suka kashe Agom Adara na kachia Maiwada Galadima , Dan sanda mai tsaron sa da kuma direban sa.
CAN a wata sanarwa data fitar ranar lahadi a Abuja ta hannun mataikin shugaban ta akan watsa labarai fasto Bayo Oladeji ta bukaci ta daina alakanta rikicin da siyasa kamata yayi ta hukumta wadanda ke da hannu a rikicin.
Kungiyar ta bukaci ayi garanbawul ga yanayin tsaro tare da sauya shugabanin tsaro na kasa.
Har ilayau ta bukaci a aiwatar da shawarwari da aka bada akan ilahirin rikicin kabilanci dana Addini a fadin kasar nan tare da hukumta wadanda aka kama da laifin kashe kashe a yankin Kaduna ta kudu shekaru biyu da suka shige.
Kungiyar CAN hakazalika tace a biya kudin diyya ga iyalen wadanda aka kashe a rikicin Addini dana kabilanci a kasar nan shekaru biyar da suka gabata.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %