Yan Boko Haram sun farma wani kauye a Borno suka sace sama da shanu Dari biyar, tumakai da sauran su.

Read Time:37 Second

A ranar lahadi hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA tace yan Boko Haram sun zo da niyyar fashi da makami a daren Asabar a kauyen Bale Shuwa dake karamar hukumar Jere na jihar Borno suka sace shanukai, tumakai da Akuyoyi.
Alhaji Garga ko-odinatan hukumar NEMA a shiyar arewa maso gabas ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Maiduguri.
Garga yace yan Boko Haram din sun afkawa kauyen Bale Shuwa da misalin karfe Bakwai da rabi na Daren Asabar.
Sun kashe wani nakasasshe , sun kona gidaje sittin da biyar kana suka sace shanu Dari biyu , Tumakai da Akuyoyi guda Dari uku.
Amma kura ya lafa harma mutanen da suka gudu daga gidajen su , sun dawo bayan sojoji sun fatattaki yan Boko Haram.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %