Wani da ake zargin barawo ne ya shiga masaukin baki na IBB ya saci waya da kudi
Read Time:31 Second
An kama wani da ake zargin barawo ne Joseph Peter ya fasa wani daki a masaukin baki na IBB dake shango , Minna jihar Niger ya saci wayar hannu , abun chajin waya da kudi naira dubu goma.
An gano cewa wata Oluwafunke Yusuf data kasance a Minna don halartan taron sanin makamar aiki ce wanda ake zargin ya fasa dakin ta ya shiga.
Yan sanda na Niger suka kama wanda ake zargin Dan asalin garin kuta a karamar hukumar shiroro na jihar.
Kakakin yan sanda na Niger Mohammed Abubakar ya tabbatar da hakan amma yace za a kai wanda ake zargin kotu bayan sun kammala. Bincike.
