Sarkin Kano ya bukaci gwamnatin Najeriya ta fiskanci Talauci da kayyade haihuwa don yaki da Boko Haram.

Read Time:38 Second

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu ya sake sabonta kira ga gwamnatin Najeriya data tinkari sabagen talauci da karuwan jama’a sosai don shawo kan yan Boko Haram.
Yace samada mutane dubu 27 aka kashe tun farkon rikicin Boko Haram a shekara ta 2009 a yankin arewa maso gabas kuma mutane miliyan 1.8 suka rasa muhallin su tundaga wancan lokacin zuwa yanzu.
Sarkin ya sake yin magana akan ikirarin da gwamnatin Najeriya da sojojin ta keyi cewa sun nakasa Boko Haram amma haryanzu kungiyar na ta kaiwa hare hare daya zamanto barazana ga fararen hula da kuma soji.
Ya yi da cewa yan kungiyar Boko Haram za su yi ta samun mutane dake kawo kan su don shiga kungiyar idan har ba a shawon kan da’awar su ba.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %