An kama mutane uku da ake zargi da masu sace mutane ne a jihar Niger.

Read Time:40 Second

Rundunar Samar da kariya da tsaro ga farar hula a jihar Niger ta kama wasu mutane uku da ake zargin masu sace mutane ne a Pandagori dake karamar hukumar Rafi na jihar Niger.
Komandar Rundunar a jihar Mr Philip Ayuba dayake nuna wadanda ake zargin wa jaridu ranar laraba yace sun Dade suna addabar mazauna yankin.
Wadanda ake zargin yace sun amince aba su naira miliyan Hudu in kuma bahaka ba za su kashe wanda sukayi Garkuwa da shi.
Komandan yace daya daga cikin su ya taba aiki da wanda suka sacen inda shanu Dari da hamsin da tumaki Dari da saba’in suka bace a hannun sa ya kara da cewa da zaran an kammala bincike za a kaisu kotu.
An kama su da waya dauke da sim kad guda shida na kanfanonin daban daban .

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %