Gwamnar jihar Benuwe ya dauka niyyar sakawa makaranya sunan marigayiya Ochanya.
Read Time:24 Second
Gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom a ranar laraba ya umurci shugaban hukumar ilimin baidaya na jihar Philip Attachin daya daukaka Martaban makarantar furamare na garin marigayiya Elizabeth Ochanya.
Ortom wanda ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yan jaridu a makurdi yace za a sakawa makarantar sunan ta.
Kuna iya tunawa cewa yar shekara goma sha uku ta mutu ne a sakamakon wasu matsaloli na rashin lafiya bayan anyi zargin cewa uba da Dan sa sun yi mata fiyade.
