Kashe Alkali: kungiyar masu sufiyo sun fadawa yan sanda da soji cewa wanda ake zargin ba Dan kungiyar su ba ne.

Read Time:1 Minute, 0 Second

Makarantar horar da masu aikin safiyo ta kasa tace babu wani daga cikin yayan ta dake da hannu wajen kashe manjo janaral idris Alkali tsohon darektan gudanarwa na hukumar soji wanda sojoji suka sinci gawarsa a wani rijiya da ba a amfani da shi a karamar hukumar jos ta kudu dake jihar.
Shugaban kungiyar a jihar filato mista Bitrus Dang ya karyata hakan a wani jawabi ga yan jaridu a jos ranar laraba bisaga wani rohoto dake cewa wani mai suna chuwang istifanus Stephen wanda safiyo ne nadaga cikin mutum bakwai da yan sanda suke nema ruwa a jallo.
Dang yace bayan sun dubu takardan rajistan yayan kungiyar da kuma yin tambaya daga bakin. Yayan kungiyar sai suka gano cewar babu wani mai irin wanan suna daga cikin wadanda ake zargin.
A wani taron manaima labarai da kakakin yan sanda na jihar Tyopev Terna sun bayyana masu sana’ar yiwa mota kwaskwarima guda biyu Da chuwang Samuel wanda akafi sani da Mourinho, Nyam Samuel wanda akafi sani da soft touch,wani manomi Pam Dung wanda akafi sani da Boss, wani direba Timothy chuin da kuma Hakimin Du-Dara a karamar hukumar jos ta kudu dake jihar filato take nema ruwa a jallo.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %