Yan sanda sun kama soja da wasu mutane goma Sha Tara da yin fashi da makami da sata a Gombe.

Read Time:44 Second
Rundunar Yan sanda a jihar Gombe tace ta kama wani soja dake barikin soja mai lamba 301 dake Gombe da laifin yin fashi da makami tare da wasu mutane goma Sha Tara da suka aika ta laifuffuka daban daban.
Komishinan Yan sandan na jihar Muhammad Mukaddas ya shaidawa Yan jaridu ranar Alhamis cewa sun kama sojan ne a ranar Laraba a kauyen Tabra dake ta hanyar baya wato Gombe bye pass.
Yace sojan ya amsa laifin sa don haka bada jimawa ba za a kaishi kotu.
Ya kara da cewa sauran mutane Tara an kama su ne da laifin yin fashi da makami, satar Babura, hadin baki da kuma aikata kisa.
Yace akwai mace guda daya a cikin su wacce ta ya sar da jaririn ta Dan wata biyar.
Komishinan Yan sandan yace dukkanin wadanda ake zargin za a kai su kotu don hukunta su.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %