Mutane uku sun kone kurmus a wani hatsarin mota a Kogi.

Read Time:47 Second
Hukumar kiyayye hatsuran kan hanya na Tarayya a Ranar Laraba tace mutane uku suka kone har lahira a wani hatsarin mota a gidan mai na total dake Ilene,jihar Kogi.
Adelaja Ogungbemi shugaban sashen hukumar a Okene yace Banda mutane ukun wasu da dama sun sami raunuka daban daban kuma motoci guda bakwai suka kone kurmus.
Yace hatsarin wanda ya faru kimanin karfe goma Sha daya da minti goma na dare a ranar goma Sha takwas ga watan Disamba a sakamakon wani babar mota shake da Kaye tana gangarowa sai burkin ta ya shanye sai ta afkawa sauran motocin.
Mr Ogungbemi yace a sakamakon hakan sai wuta ta tashi ta kona wadanda ke cikin motar.
Yana mai cewa saboda zafin wutar ya Hana gudanarda aikin ceto harya kai ga mutane ukun dake cikin motar suka kone kurmus.
Acewar sa aikin ceto ya kai su karfe goma na safe don kawarda motocin da suka tare hanya .

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %