GARIN YOBE NA CIKIN SABUWAR HAREN BOKO HARAM

Read Time:1 Minute, 10 Second
Garin Katarko dake da Nisan kilomita Ashirin a kudu kusa da Damaturu baban birnin jihar Yobe sun fiskanci hari daga wasu da ake zargin Yan Boko Haram ne.
Wanan harin na zuwa ne bayan kwana biyu da yan ta’addan suka yi kwantar Bauna wa Sansanin Sojoji dake kuka-reta mai Nisan kilomita Ashirin a gabas da Damaturu inda suka kashe sojoji goma Sha uku tare da kona Sansanin.
An gano cewa maharan sun farma kauyen da misalin karfe biyar da minti Arba’in da biyar a lokacin da ake Jin karan Harbin bindiga a yankin da sojoji suke a wajen garin.
Wani mazaunin garin Malam Muhammad Dalhatu wanda ya tsira a harin yace maharan sun zo ne a cikin mota guda goma hilux sai suka fara harbi barkatai.
Yace wasu kauyawa daga kauyen Lineri sun fada mana cewa yan ta’addan suna zuwa garin mu amma kafin mu Ankara mu kwashe iyalin mu sun Riga da sun iso sai muka watsu muka barsu a hannun Allah.
A ranar bakwai ga watan Nuwamba, 2018 kimanin wata biyu ke nan aka kai irin wanan harin a garin Katarko inda aka kona tankar yaki na sojoji da wasu kayan aiki na soja.
Duk da haka a ranar Ashirin da bakwai ga watan yuli 2014 a wani hari na uku da aka kaiwa garin yayi sanadiyar kashe mutane da yawa kuma akayi garkuwa da mata da yara samada dari.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %