MUSULMAI SAMADA DARI BIYAR SUKA YI BIKIN KIRISTIMETI A GIDAN WANI FASTO A KADUNA.

Read Time:43 Second
Musulmai samada dari biyar suka yi tururuwa zuwa gidan fasto Yohanna Buru a Jihar Kaduna don yin bikin kiristimeti a matsayin wata hanya na kara samun jituwa tsakani Musulmai da kirista.
Musulmai sun kunshi matasa, mata, limamai , kungiyoyi masu zaman kansu da masu sarauta daga jihohin Arewa da wasu makwabtan kasashen Afurka.
Zuwan su da manufar karfafa zaman lafiya,hadin kai da zumuncin addini da hakuri da juna a Jihar Kaduna da kasa baki daya.
Buru shine shugaban chochin Christ Evangelical and Life intervention Ministry yayi Addu’a samun wanzuwar zaman lafiya a tsakanin kungiyoyin addinai.
Dayeke Maida jawabi shugaban yan kungiyar yan kato da gora na jihar Kaduna Malam Muhammad Dantudu yayi rokon samun zaman lafiya da hadin kai.
Komandar CJTF yayi anfani da damar wajen yin Kira ga yan Najeriya dasu yi anfani da bikin kiristimeti don bunkasa zaman lafiya da hadin kai.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %