Boko Haram: Hukumar Sojojin Najeriya ta Hakikance cewa yan ta’addan basu fi su kayan yaki ba.

Read Time:51 Second


Hukumar Sojojin Najeriya ta karya ta cewa wai mayakan Boko Haram sun fi Sojojin ta makamai tana mai cewa furofoganda ce da kuma dakarun kashe wa makiyi jiki.

Kakakin hukumar Sojojin Najeriya Birgediya janaral Sani kukasheka Usman ya fitar yayi bayani akan batutuwa da dama tare da nuna damuwa  akan yadda wasu mahassada ke yayata labarai marasa inganci akan yaki da yan Boko Haram a Arewa maso gabas.Yace batun soja sai soja amma wasu suna soma baki a cikin harkokin soja na yaki da Boko Haram inda aka Maida shi wasan yara da kuma siyasa.Yace abun takaici wanan dakarun kashe wa makiyi jiki a fagen yaki ba wasu mahassada ne kadai ke yadawa ba harda wasu kasashen waje.

Kukasheka yace batun rashin makamai da kyautatawa Sojojin Najeriya babu buya a ciki kuma duk sadda aka gane ana daukan matakai da suka dace.Acewar sa hukumar Sojojin zata rinka magance kalubalen ta da kanta batare da wasu sun soma mata baki ko suka ko yi musu tir ba.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %