Katsina na cikin wani Hali inji Masari

Read Time:1 Minute, 57 Second

Gwamnar jihar Katsina Aminu Bello Masari yace Katsina na cikin wani Hali kuma shima kan sa bai tsira ba.Gwamna yace masu sace mutane da Barayi sun kwace jihar ya bayyana hakan ne jiya a wani zaman gaggawa akan matsalar tsaro a jihar.

Yace Katsina na karkashin Barayi da masu sace mutane ni ma kai na Gwamna ban tsira ba.

Daya ke magana kafin zaman ya shiga na sirri Masari yace Satan mutane da Barayi sun Zama ruwan dare a Katsina wanda yanzu haka yafi Satan shanu.Yace kwana biyu da suka wuce wasu mutane sun bar gida na da misalin karfe biyu na Rana wasu Yan fashi da makami guda biyar suka tare su suka masu fashi, kaga lamarin ya baci.Yace daga rohotanni tsaro dana samu daga daraktan tsaro na DSS duk sun nuna cewa akan fashi ne da Satan mutane sai dai guda daya ne kawai bai shafi hakan ba.Don haka jihar mu na cikin wani Hali shiyasa na Kira wanan zama.Babu wanda aka bari har ni kai na a gaban wanan gidan gwamnati aka sace sandan wutan lantarki guda biyar.

Wanan shine munmunar lamari da muka sami kan mu ciki kuma koda zamu kashe dare a wanan zama na yau dole mu sami mafita.

AKatsina na cikin wani Hali inji Masarin fadamin cewa anyi garkuwa da wata mata kuma suka bukaci miliyan biyar kudin amma sai suka harbe wanda yakai masu kudin.

Yace mun ga Abunda yafi haka muni a can baya kuma ya wuce yanzu ma zamu sami mafita Abunda ya rage shine kowa yayi Abunda ya dace a lokacin da ake bukata kuma a inda ake bukata.


Dole ma sami mafita don muna magana ne akan tasirin rayuwar jihar mu da jama’an ta.Zaman ya sami halartan shugabanin hukumomin tsaro, Sarakuna da shugabanin addinai.

Kakakin rundunar yan sanda na jihar Katsina Gambo Isa yace kokarin da rundunar keyi ya hada da tura jami’ai na musamman daga ofishin baban infekta yan sanda zuwa jihar don magance yan fashi da makami.Yace jami’ai yan sanda na musamman daga ofishin baban sufeton yan sanda sun kama samada mutane dari da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kwato bindigogi kala kala guda talatin goma daga ciki Kiran Ak47 ne. 

Kullum ana gabatarda da Addu’a ta musamman saboda batun rashin tsaro a Jihar.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %