Majalisar koli na kula.da Al’amurar islama ta kasa tana juyayin rasuwar shagari.

Read Time:1 Minute, 4 Second


A jiya ne majalisar koli na kula da Al’amurar islama ta kasa NSCIA karkashin shugaban ta kuma mai Alfarma sultan na sakkwato Alh Muhammad Abubakar Sa’ad na uku suka jajantawa gwamnatin Tarayya da na jihar sakkwato saboda rasuwar tsohon shugaban kasa Alh Shehu shagari.A wata sanarwa daya fitar jiya Shugaban watsa labarai na kungiyar Alh femi Abbas ya bukaci yan Najeriya dasu yi kotu da salon rayuwar shagari tare da anfani da su don cigaban Najeriya.

Abbas yace kungiyar musamman ta mika ta’aziyar ta ga iyalen marigayin da masarautar Sultan wanda shi marigayi yana daga cikin na gaba gaba kana tayi Addu’a Allah ya Raham se shi tare da baiwa iyalen sa hakurin jure zafin rashin.

Kungiyar ta ce Banda kaurin suna da shehu shagari yayi da kuma irin abubuwan alkairi daya shuka wanda yan Najeriya ba zasu manta dashi , marigayin mai son Addinine wanda kungiyar ke Alfahari dashi.

Ya tuna baya cewa Shehu shagari wanda shine zababben shugaban kasan Najeriya na farko a lokacin sa ya bada kudi naira miliyan goma, goma wa Musulmai da kirista da a Gina masallaci da Baban cibiyar ibada na kirista a Abuja.

Abbas yace wanan karamcin da shugaban kasa yayi ya Shure duk wata jita jita da ake yadawa  cewa Najeriya kasa ce ta addini guda.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %