An Sako yan kungiyar izala guda Ashirin da aka yi garkuwa da su.

Read Time:1 Minute, 10 Second


Kungiyar jama’atul izalatil Bidh’a wa’ikamatus Sunnah JIBWIS ta tabbatar cewa an Sako yan agajin ta su Ashirin da akayi garkuwa da su a ranar Ashirin da uku ga watan Disamba a jibiya, jihar Katsina.

Shugaban majalisar malamai na kungiyar Sani jingir ya bayyana hakan a wani taron manaima labarai a Jos jiya lahadi.Yace an saki yan agajin ne da misalin karfe biyu na safiyar Asabar a garin Dauran dake karamar hukumar Zurma a jihar Zamfara.

Yace an sake su ba tare da wani sharadi ba kuma wadanda sukayi garkuwa da su, sun kaisu inda suka sace su ne suka ajiye su cikin koshin lafiya.

Don yace munyi tayin Addu’a tare da rokon wadanda suka sace su cewa mu bamu da bindiga da za muyi yaki da su kuma yan agajin basu da kudi da zasu basu shiya sa Allah ya amsa mana.Ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, jami’ai tsaro SSS da yan sanda saboda nuna damuwa akan lamarin.Jingir ya bukaci Gwamnati data karawa jami’ai tsaro karfi da kuma kayan aiki don yin aiki da kyau.

Ya bukaci yan kasa da a rinka baiwa jami’ai tsaro cikakken goyon baya. A ranar talatin da daya ga watan Disamba kungiyar izala ta bada sanarwa cewa an kama yan agajin ta su Ashirin akan hanyar su na dawowa daga sakkwato bayan sun halarci kanfin na yan agaji a Dutse, Jihar Jigawa.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %