Dakarun Najeriya sun fi karfin yan Boko Haram a Damasak kana sun kashe su da yawa a Yobe.

Read Time:52 Second

A ranar Asabar Dakarun Najeriya suka fatattaki daruruwan yan Boko Haram dake son su kawo hari a Damasak garin dake Arewacin jihar Borno.Acewar rohoton jaridar Daily Trust wata majiya mai karfi na cewa yan ta’addan bangaren Mus’ab Albarnawi sun shiga garin Damasak dauke da motoci masu gurneti.

Amma Dakarun Najeriya sun yi masu kwantar Bauna bayan sun sami labarin harin da suka shirya kaiwa majiya ta kara da cewa an kashe maharan da yawa.

Wani bakauye da baya son a buga sunan sa a jarida yace maharan sun iso ne da karfe biyar da minti Arba’in da biyar kuma a cigaba da yaki har gari ya waye amma maharan basu damar shiga garin ba.

Ya ce sai a yau za a san wadanda suka mutu a tsakanin bangarorin guda biyu, wani kwararren jami’in tsaro ya tabbatar da harin. Damasak wanda a can baya yan Boko Haram suka kwace, ita cw shedkwatar karamar hukumar Mobbar a Arewacin jihar Borno, kusa da kogin Yobe da komadugu Gana wanda ke bakin iyaka da kasar Nijar.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %