Anyi Garkuwa da shugaban karamar hukumar Suleja Abdullahi Make.

Read Time:46 Second

A ranar laraba ne akayi Garkuwa da shugaban karamar hukumar suleja a jihar Niger Abdullahi Make a hanyar sa na tafiya gida daga sakatariya da yamma.
An gano cewa wasu yan bindiga ne sukayi masa kwantar bauna a motar sa na ofis kana suka fitar dashi da karfi zuwa cikin motar su kafin suka kai shi gurin da ba a Sani ba.
Anyi imanin cewa yan bindigar da suka sace shugaban karamar hukumar an danganta su ga zaben fitar da gwani da jam’iya mai mulki APC zata yi na danmajalisar wakilai na tarayya Wanda za a fara yan  sa’o’i kadan don ana zaton yana goyon bayan wani dantakara.
Yan sanda a minna ba a Iya riske su ba don samun bayani amma wani babban jami’i a rundunar yaki ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya bukaci a ga jami’in Hulda da kama ‘a na yan sanda a lokacin da jardar Thisday ta tuntubeshi.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %