Fiyade: Yan Najeriya sun bukaci Adalci wa yar shekara goma sha uku Ochanya Ogbaje.

Read Time:1 Minute, 48 Second

Yan Najeriya musamman ma masu rajin kare yancin Dan Adam sun bukaci ayi Adalci wa yar shekara goma sha uku Elizabeth Ochanya Ogbaje wacce ta mutu a karshen mako.
Ochanya tayi fama da ciwon yoyon fitsari da kuma sauran lalura na rashin lafiya a asibitin koyarwa na jihar Benuwe saboda ta sha wahala a hannun Andrew Ogboja shugaban sashen koyar girke girke na makarantar kimiya da fasaha na jihar Benuwe da kuma Dan sa Victor Inalegwu Ogboja dalibi dake mataki na karshe a fannin nazarin kiwon lafiyar dabbobi na jami’ar nazarin aikin noma na tarayya dake makurdi yayinda suka ta keta haddin ta.
Su biyu sun cigaba da kwanciya da Ochanya daliba a kolajin mata dake Gboko tun tana da shekara Tara har ta kai shekara goma sha uku.
Baban kotun yanki na daya dake makurdi, Jihar Benuwe karkashin mai shara’a S D Kwen a watan Agusta ya bada umurnin a daure Mr Agboja a gidan kaso saboda aika ta laifin hadin baki da kuma yiwa karamar yarinya fiyade.
Kotun ta sake fadi cewa mijin yar uwan yarinyar Mr Andrew Ogboja ya kwanta da Ochanya tare da Dan sa , a bincike da yan  sanda sukayi sun kama Mr Andrew tare da yaron sa Victor wanda daga suka amsa laifin su amma sun bukaci kotu tayi masu sassauci.
Mai shara’a S D Kwen yaki yaji kukan su sakamakon hakan sai ya umurci a daure Mr Andrew a gidan yarin tarayya dake makurdi har sai zuwa lokacin da aka gama shara’a.
Malamin dai ance an bada belin sa ba tare da amincewar iyalen yarinyar da aka yiwa fiyade ba kuma tun daga wanan lokaci ya gudu.
Da suke tir da wanan ta’asar kungiyar tsofoffin dalibai na mata na tarayya dake Gboko zata gudanar da zanga zanga akan abun takaicin .
Shima daya ke magana akan lamarin kansila mai wakiltar mazabar Eke a Benuwe Honarabul Dan Atayi yayi kiraga yaya maza da mata na Benuwe da sauran yan Najeriya musamman ma mata dasu sa baki don ganin cewa an kamo wadanda suka aikata laifin sun fiskanci hukumci.
Da aka tuntubi hukumar yan sanda na jihar Benuwe cewa suka yi maganar bashi a hannun su.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %