Sojojin Najeriya sun kwato Mata goma sha biyar da yara daga hannun Boko Haram.

Read Time:41 Second

Sojojin Najeriya dake karkashin operation Lafiya dole sun yi gamo da Boko Haram a yankin Ngoshe dake Borno sun kubutar da mata goma sha shida  da yara daga hannun su.
Dakarun dake karkashin lamba 82 a Ngoshe tare da hadin hannun yan kato da gora suka fatattaki Boko Haram a yankin Agapaluwa dake Ngoshe sai suka ga mata shida da yara goma.
Acewar sojojin sun harbi biyu daga cikin yan kungiyar kana saura sun gudu da ciwon da suka samu ta hanyar Harbin su .
Mata da yaran da aka kubutar da su an kaisu wani guri da ba a bayyana ba don tantance su tare da sanin asalin su.
A ranar Talata sojin Najeriya suka tabbatar da kubutarwan a zauren ta na tweeter kana tace sun kona kayan abinci da suka samu a mabuyan yan Boko Haram.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %