Wasu yan bindiga dadi sun kashe jigon jam’iyar APC , suka raunata matarsa da yara.

Read Time:50 Second

Wasu tsageru da ba a san ko su wane ne ba sun kashe wani jigon APC a Abuja Fasto Benjamin Imeogu kana suka raunata matar sa da yaran sa dake gurin da abun ya faru.
Imeogu Wanda shine shugaban komitin gudanarda zaben fidda Dan takara na majalisar tarayya na APC a Abuja an harbeshi sau biyar a kirjin sa akan hanyar zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja ranar Alhamis da karfe Tara da rabi na dare.
Har’ilayau rohoton ni sun nuna cewa matar marigayin da daya daga cikin yaron sa sun sami munmunar rauni saboda an harbe su a ciki, sauran yara biyun kuma sun tsira da kananan rauni saboda Harbin bindiga.
An ajiye gawar imeogu a dakin ajiye gawa dake Baban Asibitin Abuja kana matar sa da yaro suna fama da rayuwar su a wani asibiti da ba a bayyana sunan sa ba.
Kakakin yan sanda na Abuja DSP Anjuguri Manzah yayi alkawarin zai bada Karin bayani akan lamarin amma haryanzu shiru.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %