Gobara ta kama kasuwar Kano.

Read Time:39 Second

Hukumar kwana kwana ta jihar Kano tace gobara ta kona Wasu shaguna na wucin gadi guda 77 a kasuwar yan kurmi(Gumama) a jihar Kano.
Kakakin hukumar kwana kwana na jihar Alhaji Saidu Muhammadu a wani rohoto daya baiwa yan jarida ranar lahadi yace 70 daga cikin shagunan sun kone kurmus, guda bakwai sun tsira saboda dauki da yan kwana kwanan su kai.
Muhammad ya shawarci yan kasuwa dake kasuwar da kuma mazauna yankin da suyi hattara tare da daina yin amfani da duk wani Abu da zai haddasa gobara a lokacin kaka.
Ya kara da cewa haryanzu ana kan binciken musabbabin gobarar kana ya shawarci jama’a da su rinka Adana bokiti, bargo da kuma abun kashe gobara don yin amfani da su kafin yan kwana kwana su zo.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %