Ma’aikatan hukumar Zabe INEC guda Hudu, wakili a hukumar NYSC da yarinya yar shekara uku sun mutu a hatsarin mota a kogi.

Read Time:43 Second

Ma’aikatan hukumar zabe na kasa guda Hudu , wani wakili a hukumar NYSC da yarinya yar shekara uku sun mutu a hatsarin mota akan hanyar Ajakuota zuwa Lokoja ranar asabar.
Wadanda abun ya Shafa suna dawo wa ne daga Aiyingba, Jihar kogi bayan sun halarci bikin aure na wani ma’aikacin su.
Rohoton na cewa Dan yiwa kasa hidimar yana aiki ne da ofishin zabe na Lokoja yarinyar kuwa na daya daga daga cikin ma’aikatan hukumar zaben ne.
Darektan watsa labarai da ilimantar da masu jefa kuri’a na hukumar zabe na kasa a jihar kogi, Ahmed Biambo ya tabbatar da aukuwar lamarin a hira da akayi dashi ta wayan tarho yace wadanda suka mutun ma’aikata ne a sashen fasahar sadarwa da kuma sashen kudi na ofishin hukumar zabe na kasa.
Bimbo yace an zuba gawawakin su a dakin Adana gawa dake asibitin tarayya dake Lokoja.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %