Wani mutum ya kashe kan sa a layin dogo na Abuja.

Read Time:52 Second
Wani mutum mai matsakaicin shekaru wanda haryanzu ba a San sunan sa ba ranar litinin ya tsaya akan layin dogo kuma jirgin kasa ta haushi a yankin phikwore, kubwa Abuja.
Acewar kanfanin dillancin labarai NAN tace mutum da aka ganshi a kwance akan layin dogo yana jiran jirgi tazo ta haushi ya kuma bar wasiya cewa zai kashe kan sa.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe goma Sha biyu da minti Arba’in da biyar na Rana yan kilomita kadan da tashar dogo na Kubwa.
Mutumin ya bar wasiya a takarda cikin jaka dake dauke da sutura daya ajiye a gefen layin dogon.
Acewar wasu shaidun gani da Ido sun shaidawa NAN cewa wasiyar cikin takaitaccen rubutu ya barwa mata da yayan sa cewa suyi hakuri su yafe shi don bashi da kudin da zai Kula da su.
Daya ke tsokaci akan lamarin kakakin hukumar Kula da harkokin sufurin jiragen kasa NRC Mr Niyi Ali ya tabbatar da hakan amma yace Ana kan gudanarda bincike don dalilin daya sa mutumin ya kashe kan sa.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %