An yanke wa wani hukuncin daurin wata uku a Gombe saboda danfara bada aiki

Read Time:1 Minute, 6 Second

A ranar Talata babar kotu dake Gombe ta yanke wa Raymond sule hukuncin daurin wata uku saboda ya karbi naira dubu dari da Hamsin cewa zai baiwa wani aiki.

Hukumar EFCC tace Raymond ya karbi kudin ne a hannun yaron manomi Daniel Solomon don bashi damar shiga aikin soja.Kakakin hukumar EFCC Toni Orilade ya bayyana hakan a wata sanarwa a Abuja.

Yace Raymond ya fara tafiya gidan yari ne tun a ranar Ashirin da bakwai ga watan Augusta 2017 bayan ya karbi kudin daga hannun yaron Solomon wanda ya turashi yaje Kaduna ya sami jami’in daukar aikin a Zaria.

Orilade ya ce bayan ya kashe kwana uku a Zaria sai yaron manomi ya gane cewa lambar waya da Raymond ya bashi bana jami’in ba ne nashi ne.

A saboda kwararan shaida da aka gabatar akan bai bata wa kotu lokaci ba inda ya amsa laifin sa.

Jami’i mai shigar da kara Ndeh Godspower ya bukaci kotu data daure shi daidai da dokar laifin da ake tuhumarsa.Sai dai kuma lawyan sa ya roki kotu data yi masa sassauci.

Alkalin kotun mai shara’a Muhammad ya yanke masu hukuncin daurin wata uku ko kuma ya biya kudi naira dubu Arba’in tare fa bada umurnin da a karbi kudin daya karba a hannun manomin daya danfara don a Maida mishi.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %