Jirgi mai saukar Angulu MI- 35 da yayi hatsari: Rundunar Sojojin sama sun binne jami’ai guda hudu

Read Time:44 Second

A jiya ne rundunar Sojojin sama ta binne gawar jami’ai guda hudu da sukayi a jirgin sama mai saukar Angulu MI-35 da yayi hatsari a Damasak, jihar Borno ranar biyu ga watan junairu.

An binne su makabartan Sojoji na kasa dake Abuja bisaga Al’adar sojoji bayan Addu’a a chochi da kuma gabatarda Sallah jana’iza.

Wadanda aka binne da Akwai shugaban su flight lieutenant Perowei Jacob, sai mataimakin sa kaltho Paul kilyofas, Sargeant Auwal Ibrahim, Lance corporal Adamu Nura da Meshark Ismael.

Baban hafsan Sojojin sama Air vice Marshall sadique Abubakar yace jami’ai sun rasa rayukan su ne a lokacin da suka bi motocin yan ta’adda don kare rayukan sojoji na bataliya 145 dake Damasak a Jihar Borno.

Yace mutuwar jami’ai zai kara masu , su da suke raye kwarin gwiwa da kuma jajar cewa wajen yaki da tona Asirin masu tada kayar baya da kuma tsautsauran ra’ayi.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %