BENUWE: SARKIN TIVI YA TSINEWA YAN SIYASA

Read Time:1 Minute, 7 Second

Shugaban majalisar Sarakuna na jihar Benuwe Tor Tiv furofesa James Ayatse ya aza tsinuwa akan duk wani Dan siyasa dake kokarin haddasa fitina kafin, lokacin da kuma bayan Baban zabe na wanan shekara.

Sarkin ya aza tsinuwa ne jiya yayinda yake magana a gurin bikin rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman tsakanin yan takaran kujeran Gwamna a Jihar bikin da hukumar zabe na kasa mai zaman kanta ta shirya a Makurdi.

Sarkin wanda ya bukaci yan siyasa da su kauracewa duk wani da kan iya haddasa rikici a Jihar, yace babu wani Abunda ya fi zaman lafiya.Sarkin Tivi yace jihar Benuwe na bukatar zaman lafiya fiye da kowacce jiha a kasar nan bayan halin data shiga a shekara daya baya don haka shirin yayi daidai.

Yace masarautar tana Maida hankali akan zaman lafiya saboda ita abun zaifi shafa don haka duk mutumin da zai kawo mana fitina ba za mu barshi ba.

Mu Sarakuna muna zama da jama’a kuma mun san ciwon su , kuma mu kan ji zafi idan babu zaman lafiya, don haka a Shirye muke da muyi komai don zaman lafiya a Jihar mu.

A dalilin haka muka cire Bakin mu daga siyasa don mun Sha wuya sosai shiya sa wanan bikin yana da muhimanci da kuma Abunda zai biyo baya bai kama yarjejeniyar zaman lafiya ya kasance a takarda ba kawai.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %