Jirgi mai saukar Angulu na sojoji Najeriya yayi hatsari a yaki da Boko Haram

Read Time:53 Second

Jirgin helikofta na sojin sama a Najeriya yayi hatsari a yaki da Boko Haram a Daren Laraba, jirgin an ce yana bada taimako ne ga Sojojin dake da zama a Damasak mai lamba 145 bataliya a Arewacin jihar Borno.

Daraktan watsa labarai na rundunar Sojojin sama ibikunle Daramola ya bayyana hakan sai dai yaki yafi wani irin sanfuri ne kuma jami’ai nawa ne a cikin jirgin da yayi hatsari.


Rundunar Sojojin sama a Najeriya nada jirage masu saukar Angulu da yawa bugun kasar Rasha.

Daramola yace jirgin na daga cikin wanda ke yaki da Boko Haram a Arewa maso gabas.

Ya kara da cewa hatsarin ya faru ne ranar biyu ga watan junairu na sabuwar shekara da misalin karfe bakwai da minti Arba’in da biyar kuma babu wani cikakken bayani akan makasudin hatsarin amma da zaran an samu zamu gaya wa jama’a.

An samu Ā hasarar ce bayan yan wasu sa’o’i da Daramola ya fadawa jama’a cewa jirgin yakin da karkashin operation lafiya dole ya ragargaza wani guri da yan Boko Haram ke ganawa kusa da Baga.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %