Yan bindiga sun sace wani Dan kasuwa a kebbi.

Read Time:48 Second

Rohoto na cewa an wasu yan bindiga su sace wani babban Dan kasuwa kuma mai Harka sai da zannuwa Alhaji Murtala Zauro a jihar Kebbi.
An sace shi ne a Daren lahadi bayan ya idar da sallah da karfe takwas a kauyen sa Zauro, garin dake kan hanyar zuwa Birnin kebbi da Argungu.
Wani dangin sa wanda ya tabbatar da hakan amma ya nemi a sakaye sunan sa yace bayan sun idar da sallah isha’i sai ya shiga gida dake daura da masallacin, sai ya sami sako cewa wasu a motar fijo 406 suna son ganin sa kuma suna jiran sa a waje.
An ce Dan kasuwan yana da manyan shaguna guda uku a cikin Babbar kasuwar Birnin kebbi, yana da mata biyu da yara.
Ya kara da cewa Wanda suka yi Garkuwa dashi haryanzu basu tuntubi iyalin sa ba.
Jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sanda na jihar kebbi DSP Danjuma possible ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %