Yarbawa sun koka da yadda yan uwansu ke hasarar dukiyoyin su saboda rikicin Jos

Read Time:39 Second

Yarbawa dake Arewancin Najeriya sun koka da yawan rikici a Jos, jihar filato Wanda ke haddasa rasa rayuka da dukiyoyin su.
A makon jiya rikici ya barke a jos yayi sanadiyar mutuwar mutane da yawa.
Wadanda abun ya fi Shafa sune mazauna unguwoyin Nasarawa Gwom, Tina junction, Angwan Rukuba da Dutse ukun inda yarbawa suka fi yawa.
A wata sanarwa shugaban kungiyar Alhaji Abdulhakeem Ayinde Aka yace yarbawa basu ji dadin yawan rikici inda ake farma mutanen su wadanda yan kasuwa ne kuma an San su da son zaman lafiya da bin doka.
Yayinda yake yabawa Gwamnatin jihar, jami’an tsaro, shuhabannin Al’uma dana Addini saboda kwantar da tarzomar na baya bayan nan Aka ya bukaci masu ruwa da tsaki da a kodayaushe su kasance masu hub asa don magance faruwa mumunar lamarin.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %