Yan sanda na nemar wata yar aiki da ta kashe uwar dakin ta.

Read Time:33 Second

Yan sanda suna Neman wata yar aiki Becky Johnson wacce ake zargin ta da kashe uwar dakin ta Yemisi Haasz a gidan ta dake Asokoro Abuja kuma tayi gaba da dukiyoyin matar da ta kashe.
Jami’in Hulda da jama’a na hukumar yan sandan Abuja Anjuguri Mamza yace yan sanda suna aiki akan karar ya kara da cewa ana kan kokarin kama mai laifin.
An binne Haasz ranar laraban makon jiya a makabartan Apo, Abuja.
Acewar sa yar aikin data gudu bayan ta kashe uwar dakin ta ta rufe gawar ta a cikin daki tare da yar ta sannan ta gudu da sarkokin gwal, kudin kasashen waje, wayoyin hannu da suma.

Loading

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %