IBB: abun da yakamata sojojin suyi akan rashin tsaro.
Read Time:32 Second
Tsohon shugaban kasa na soji a Najeriya janaral Ibrahim Badamasi Babangida IBB ya bukaci kolajin tsaro na kasa data gaggauta bullo da wata tsari da zai inganta shugaban ci nagari da tsaro a Najeriya.
Ya bayyana hakan ranar Talata a lokacin da tawagar mahalarta kolajin tsaro na kasa suka kai masa ziyara a gidan sa dake Minna, jihar Naija.
Babangida yace lokaci yayi da sojojin Najeriya zasu yi zurfin tunani akan yadda zasu fitar da dabarun magance kalubalen rashin tsaro a Najeriya.
Shugaban tawagar komodo Solomon Agada ya shaidawa Babangida cewa rangadi da suka kawo jihar Naija don samun bayyanan farko da manufar magance kalubalen kasa.
