Ruwa yaci yara guda goma Sha Tara a Kwara.
Read Time:36 Second
Akalla yara guda goma Sha Tara ruwa yaci su ranar asabar a wani hatsarin jirgin ruwa dake dauke da su don sallaka da su kogin Niger yayinda zasu bikin auren gargajiya a wani gari dake jihar Niger.
Jirgin ruwan na dauke da mutane ashirin da biyu yawancin su yara ne sai ya kife , an cechi guda biyu saura goma Sha Tara ruwa ya tafi dasu kuma sun mutu.
A halin da ake ciki sakataren masarautar lafiagi Alhaji sulaiman Aliyu ya tabbatar da hatsarin.
Hakazalika kakakin rundunar Yan sanda a jihar Kwara DSP Ajayi Akasanmi ya tabbatar da lamarin.
Ya shaidawa kanfanin dillancin labarai NAN cewa jami’ai da sauran hukumomin tsaro sun taimakawa mutanen kauyen wajen gano gawawwakin yaran
