An tura Dan sanda daya kashe yar uwan tsohuwar minista zuwa gidan yari.

Read Time:43 Second

A ranar juma’a yan sanda suka garfanar da mataimakin sufiritandan yan sanda Inagozie Godwin a gaban Baban kotu na Zuba, Abuja saboda laifin kashe Miss Anita Akapson yar war tsohuwar ministan kudi Nenadi Usman.
Godwin yace baiyi laifi ba yayinda aka karanta masa laifin sa na aikata kisa a gaban mai’shara’a A O Ebong ranar juma’a.
Dan sanda mai gabatarda kara Donatus Abbah yace Godwin ya harbi Miss Akapson mai shekara talatin da daya da misalin karfe Tara da minti Arba’in da biyar na dare a yankin katampe ranar goma sha uku ga watan oktoba kuma ya aikata laifin kisa daya kamata a hukunta shi daidai da doka mai lamba 22(3) da 24.
Alkalin kotun yace laifin son aikata kisa hukuncin sa bana kashe wa ba ne sai dai daurin rai da rai a gidan yari.
An daga karan zuwa ranar 29 ga watan Nuwamba

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %