Sojojin Sama sun fatattaki Boko Haram a Talala , jihar Borno

Read Time:34 Second

Rundunar Sojojin sama  a karkashin operation Lafiya Dole sun yi ruwan boma bomai akan yan Boko haram a Talala jihar Borno.
Darektan Hulda da jama’a da watsa labarai na sojan sama dake Abuja Ibinkule Daramola ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar ranar Asabar a Abuja yace an gudanarda aikin ne ranar juma’a.
Daramola yace an gudanarda aikin biyo bayan sahihan rohotanni cewa Boko haram ta fara sauyawa mayakan ta guri daga yankin tafkin chadi a arewacin Borno zuwa bude sabbin sansani a yankin Talala zuwa Ajigin da Buk dake jihar.
Kakakin sojin sama yace sojin sama suna aiki dana kasa don tabbatar da sun kakabe raguwar yan Boko haram a jihar Borno

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %