Matasa sun kona gidaje a filato saboda sakamakon zabe.
Read Time:39 Second
A ranar Alhamis ne wasu tsagirun matasa suka kona gidaje Hudu a karamar hukumar Langtang da kudu a sakamokon zabe na kananan hukumomi da aka gudanar ranar laraba a jihar filato.
Matasan sun fusata ne a lokacin da Gwamna Simon Bako lalong ya bada sanarwa a gidan Radiyo cewa za a ransar da wadanda suka ci zaben da karfe biyu yayinda su matasan ke jiran baturen zabe ya karbi sakamakonnin zabe da aka gudanar a gundumomi.
Wani shaidar gani da yace gidajen da aka kona mallakar jami’in daya gudanar da zabe a yankin Mr Andrew Sambo da wani fitaccen Dan siyasa a yankin Mr Jackson Ponzhi.
Dayake tabbatar da aukuwar lamarin kakakin yan sandar jihar filato Terna Tyopev yace shima ya samu labarin amma har yanzu bashi da cukakkun bayanai akai.
