Wani Dan nijar ya dabawa wani wuka harya mutu a jigawa.
Read Time:34 Second
Hukumar kula da harkokin shige da fice ta kasa ta kama wani Dan nijar isa idirisu saboda ya caki wani mutum da wuka harya mutu a Hadeija , jihar Jigawa.
Shugaban hukumar a jihar Alh Garba Abdul ya shaidawa yan jaridu yayinda yake bayyana mai ladin a Dutse ranar Talata.
Garba yace wanda ake zargin ya dabawa Suleiman Adamu wuka a kofar gidan talba dake cikin barin hadeija kuma ya mutu a shekara ta 2008 kana ya gudu zuwa garin su Nijar.
Wanda ake zargin jami’an hukumar NIS ne suka kama shi bayan dubu ta cika dashi a Maigatari zuwa Gumel bakin iyakar Najeriya da Nijar.
Garba yace an same shi da guraye da magungunan tsafi.
