BOKO HARAM SUN KAI HARI WA SANSANIN SOJOJI DAKE BORNO SUN KASHE SOJOJI DA DAMA

Read Time:1 Minute, 28 Second
Wasu da ake zargin yayan kungiyar Boko Haram sun kai hari a wani Sansanin Sojoji dake jihar Borno a karshen mako inda suka kashe sojoji da dama wasu kuma sun bace.
Acewar kanfanin watsa labarai na Sahara reporters yan ta’addan sun kai harin ne a Gudunbali  dake Garin Guzamala suna kan motocin sojoji mai dauke bindigogin Harbin jirgin sama sai suka bude wuta ma Sojojin.
Wani majiya na cewa Sojoji da yawa sun mutu saboda yan Boko Haram sun zo da yawa amma tunda farko Sojojin sun yi na maza amma da suka ga yan Boko Haram sun fi karfin su sai suka gudu zuwa cikin daji inda wasun su suka kwana a cikin dajin daga ranar juma:a zuwa Asabar, bukatar su shine su kashe sojoji kawai ba ruwan su da fararen hula sai dai wadanda ke aiki da Sojojin.
Wani soja daya ga harin amma ya nemi a sakaye sunan sa yace yan ta’addan sun kware.
Yace sun karfin mu saboda ba irin yan Boko Haram da muka saba fada da su bane wadannan sun iya rike bindiga da harbi cikin kwarewa da za mu iya fin karfin su amma harsashin mu ya fara karewa bamu da wata zabi sai muka gudu wasun mu suna Damasak.
Yan ta’addan sun cigaba da kai hare hare a garin kukawa inda suka afkawa Sojoji da ofisoshin yan sanda tare da fatattakar jami’ain tsaro kuma suka kwashe tirelolin abinci kana suka kona Sansanin Sojoji dake Kukawa.
Muhammad kormi mazaunin yankin da yayi gudun hijira zuwa Maiduguri yace yanzu babu sojoji a kukawa duk sun janye kodashike damuwar su sojoji ne babu ruwan su da fararen hula amma ba mu yarda da su ba shiya sa mutanen kukawa ke tserewa daga yankin don babu tsaro.
Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %