Kungiyar lauyoyin Najeriya NBA ta gargadi rundunar soji dasu bi ka’idar aiki ayayinda suke Neman janaral daya bace idris Alkali a yankin Dura- Du jos, jihar filato.
Read Time:25 Second
Ta kuma yi tir da sabon rikici a jos inda ta bayyana a matsayin abun takaici kuma babbar koma baya ga samun cigaba ko ta wani fuska a jihar.
Wanan na zuwa ne a lokacin da sojojin suka kyallace wata mace mai tsohon ciki Noro Dung wacce lokacin haihuwar ta ya wuce da sati biyu amma sojojin suka kama ta a lokacin da suka kai tsumame.
Ana zargin cewa an kama Noro ce da uwar mijin ta tsohuwa kuma taji ciwo kana tana bukatar kulawa.
