Gwamnatin jihar Gombe ta karbi tallafin dalar Amurka muliyan 10 don kare cutar Tamowa.
Read Time:27 Second
Bankin duniya ya bada tallafin dalar Amurka miliyan 10 wa gwamnatun jihar Gombe don magance matsalar cutar Tamowa .
Babban sakatare a ma’aikatar ilimi a jihar Steven Danladi ya bayyana haka a taron tattaunawa tsakanin gwamnati , majalisar Dokoki da kafoffin watsa labarai akan kasafin kudi na abinci masu Gina jiki a jihar.
Taron wata jungiyar farar hula wato CISLAC a shirya a Gombe ranar juma’a.
Yace jihar na daga cikin jihohi 12 da suka sami kudin tare basu miliyan Hamsin duk shekara har na shekaru biyar don karfafa aiwatar da shirin a jihar .
