Yan Asalin garin Bokkos sunyi yunkurin kawo karshen hare hare da Fulani ke kawo wa jami’ar jihar Filato.

Read Time:37 Second

Saf Bature Dakta John Gabriel Mallo Makwal ya tabbatar wa hukumar gudanarwan jami’ar jihar Filato, Bokkos cewa matsalar rashin tsaro a yankin ya kusa ya zo karshe saboda majalisar masarautar sa da Fulani makiyaya suna kokarin kulla yarjejeniyar zaman lafiya atsakanin su don karshen yawon rikici da makiyaya da kabilun Bokkos.
Makwal ya bada tabbacin hakan yayinda shugaban jami’ar jihar Filato shehun malami Yohanna Daniel Izam ya jagoranci hukumar gudanarwan jami’ar izuwa gaisuwar ta’aziya wa sarkin saboda rasuwar yar sa.
Ya tabbatar wa shugaban jami’ar cewa matsalolin rashin tsaro a yankin zai kare kwanan nan don masarautar zata sa baki kuma asibitin da ake rikici akan filin ginawa za a Gina harma ya zamonto asibitin koyarwa don biyan bukatar malamai, dalibai da kuma masu gari.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %