Akwai alamun cewa mataimakin Gwamnar jihar Sokoto ya sauka daga mukamin sa.
Read Time:22 Second
Ana zargin cewa mataimakin Gwamnar jihar Sokoto Alhaji Ahmed Aliyu ya sauka daga kujerar.
Mataimakin Gwamnan shine dantakaran Gwamna na APC a jihar wanda ake ganin zai kara da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da wata kila ya zama dantakaran Gwamna na PDP a zabe na dubu biyu da shatara.
An ce Ahmed ya mika takardan ajiye aiki wa majalisar dokokin jihar ranar Talata amma yan majalisar basu karanta wasikar ba yayinda sukayi zama.
