Tafiya yiwa Kasa Hidima : Dalibai sun koka da haramtawa Jami’o-in su fafatawa a shirin.
Read Time:39 Second
Hukumar shirin yiwa kasa hidima NYSC ta haramtawa jami’ar jihar Benuwe dana Ayyukan gona na tarayya daga tura daliban su zuwa shirin matasa masu yiwa kasa hidima , na shekara daya.
Shirin ya haramta wa makarantun ne na shekara biyu saboda sakaci da kuma cuwar cuwar rage shekaru.
A martanin sa shugaban jami’ar jihar Benuwe Shehun Malami Moses Kembe a wata zama da sukayi yayi roko da ayi masu rangwami.
Kembe a zaman da aka tashi babu dacewa yace babu ruwa hukumar gudanarwa da cuwa cuwar rage shekaru , daliban ne da Kansu ke aikata hakan.
Rokon da Kembe yayi bai samu karbu wa ba domin kuwa hukumar shirin NYSC ta dage cewa hanyar data dace su hukumta jami’o-in da abun ya Shafa ta hanyar daliban su shigar manhajar shirin.
