An harbi mutum uku yayinda kungiyoyin maitar zamani suka kara da juna a Otukpo, jihar Benuwe.

Read Time:39 Second

An harbi mutum uku yayinda kungiyoyin maitar zamani suka kara da juna a Otukpo, jihar Benuwe.
A ranar juma’a wasu kungiyoyin maitar zamani guda biyu dake kishi da juna suka kashe mutum uku daga ciki akwai Ochoche Dickson iduh wanda ya kammala yiwa kasa hidima ke nan a titin Asoka/Ojira a Otukpo,jihar Benuwe.
Wani shaidar gani da ido yace yakai makonni da dama suna fada da juna kafin harin na ranar juma’a kuma sati uku da suka gabata sun kashe mutum uku.
An gano cewa wanda aka kashen yana daga cikin rukunin yan yiwa kasa hidima da suka gama ke nan kuma ya tafi Otukpo don ya nuna wa iyayen sa takardan shaidar gama yiwa kasa hidima shine ya gamu da ajalin sa ta hanyar harbe shi.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %