Wasu yan baranda sun kashe Dan sanda da wasu mutane biyar a Zamfara.

Read Time:37 Second

A ranar juma’a ne aka kashe akalla mutum shida daga ciki da akwai Dan sanda mai igiya biyu da wasu yan baranda suka kashe a kauyen Gurbin Bore, karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
Kakakin yan sanda na jihar SP Muhammad Shehu yace yan barandan wanda sun kai Dari sun kai hari wa kauyen ne da masalin karfe goma na Daren juma’a.
Yace mutum uku sun ji rauni sosai kuma an kaisu Asibiti suna karnan magani.
Shehu ya kara da cewa yan bindigan wanda ake zaton sun fito ne daga dajin Dumburum sun gamu da tirjiya daga jami’an tsaro na hadin gwiwa da suka fatattake su.
Amma ya tabbatar cewa ana bin sawun barayin kuma za a kama su don su fiskanci hukumci.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %