An kashe yan Shi’a guda uku a wani fada da Sojoji.

Read Time:36 Second

James Myam, komandan barikin sojoji na Garrison dake Abuja ya tabbatar cewa an kashe yan Shi’a guda uku a wani rikici da sojoji ranar Asabar a yankin Zuba dake Abuja yayinda sojoji guda biyu suka ji ciwo.
Mr Myam wanda Manjo janaral ne yace sojojin barikin Garrison yan Shi’a suka afka masu a gadar Zuba yayinda suke rakiyar Albarusai da makamin kare dangi daga Abuja zuwa Babar cibiyar Adana albarusai na soji dake Kaduna.
Sai dai kuma yace kura ta lafa kana ya shawarci jama’a musamman masu bin hanyar Abuja zuwa Zuba da su cigaba da harkokin su.
Komandan sojin ya tabbatar da cewa babu wani mahaluki da za a barshi ya tada zaune tsaye ko kai hari wa tawagar soji.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %