Mataimakin sekataren watsa labarai na APC Wanda ya sauka kwanan nan Timi Frank a cikin wata budediyar wasika ga Baban sekataren majalisar dinkin duniya
Read Time:38 Second
Antonio Gutteres ya bukaci a kafa hukumar bincike na kasa da kasa akan kashe yan Shi’a da jami’an tsaro keyi a Najeriya.
A cikin budediyar wasikar daya aikawa ofishin jakadancin Amurka, ingila da tawagar kungiyar tarayyar turai , jamus da faransa Frank yace kashe yan Shi’a babu Adalci aciki.
A cikin budediyar wasikar da ya sake baiwa yan jaridu tsohon kakakin APC yace kisan ya zamanto alamace ga irin yadda wannan gwamnatin bata daraja yancin Dan Adam.
Yace lamarin da ake barin jami’an tsaro suna bude wuta ganin damar su ga yan Najeriya dake zangar zangar lumana ba tare da makami ba ya nuna yadda ake amfani da jami’an tsaro don aikata ba daidai ba wanda acewar sa bai kamata a cigaba da barin hakan yana faruwa ba.
