Hukumar Sojojin Najeriya sun kunce Bom daga jikin wata mace yar kunar Bakin wake A Adamawa.
Read Time:26 Second
Dakarun bataliyar sojoji mai lamba 143 dake gudanarda bincike a Gulak , jihar Adamawa sun kunce bam a jikin wata yarinya yar kunar Bakin wake data saka a jikin ta don ta dashi a kauyen Dar da sanyin safiyar ranar 26 ga watan Disamba.
Sojojin Najeriya suka bayyana hakan a manhajar ta na Twitter.
Dakarun tare da hadin hannun mafarauta da yan banga sun gaggauta kellache gurin da abun ya faru tare da yin tsintiri a garin don tabbatar da babu saura ko kuma yan boko Haram.


